
Rundunar yan sandan jihar Sokoto ta haramta duk wani gangami ko jerin gwano gabanin ko kuma bayan sanar da hukuncin shari’ar zaÉ“en gwamnan jihar da za ayi a ranar Asabar.
Kwamishinan yan sandan jihar Sokoto , Ali Kaigama shi ne ya fadi haka cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Ahmad Rufa’i ya fitar a ranar Juma’a.
Sanarwar ta ce rundunar ta samu bayanan cewa wasu sun kuduri aniyar yin jerin gwano ko kuma nuna murna ga hukuncin kotun.
Kasancewar jihar Sokoto jiha ce da aka santa da zaman lafiya rundunar ta ce baza ta bari ayi wani taro ba da ta ya saba doka ko wanda zai kawo tashin hankali.