WASHINGTON, DC —
Alhaji Isa Sanusi Bayero wanda aka fi sani da Isa Pilot, ya kwashe shekaru da dama yana aikin tukin jirgin sama gabanin ya zama sakataren sarkin Kano a zamanin marigayi Alhaji Ado Bayero kafin daga bisani ya yi murabus wani lokaci cikin wannan shekara.
Da almurun asabar din makon jiya ne, wasu mutane su biyar dauke da bindigogi suka je gidan Alhaji Isa Sanusi Bayero dake Unguwar Sharada Phase one a nan Kano da nufin kawar da rayuwar sa, kamar yadda ya shaidawa Muryar Amurka.
Yanzu haka rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano tace tana gudanar da bincike da nufin zakulo wadanda ke da hannu ga wannan yunkuri na kisan gilla, kamar yadda kakakin rundunar SP Magaji Musa Majiya ya tabbatar.