An ƙona sakatariyar ƙananan hukumomi 2 a jihar Rivers

Wasu da ake kyautata zaton ɓatagari ne sun ƙona wani sashe na sakatariyar ƙananan hukumomin Eleme da Ikwerre dake jihar Rivers.

Ƙona ginin na zuwa ƙasa da sa’o’i 24 bayan da Babban Sifetan Ƴan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun ya bayar da umarnin janye ƴan sandan dake gadin ginin sakatariyar ƙananan hukumomin.

Grace Iringe-Koko mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Rivers ce ta bayar da sanarwar janye jami’an ƴan sandan.

Wasu daga cikin zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomin da kansilolinsu  da aka zaba ranar Asabar sun isa harabar sakatariyar inda suka iske ɓakin hayaki na tashi a inda yakamata ace ofishinsu ne.

Akwai rahotanni dake cewa wasu daga cikin ƴan siyasar jihar dake adawa da gwamna,Siminlayi Fubara na da hannu a ƙoƙarin tayar da tarzoma a jihar.

A ranar Asabar ne aka gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a jihar ta Rivers inda jam’iyar APP da gwamnan jihar ke marawa baya ta lashe kujerun ƙananan hukumomin jihar guda 23.

Related Articles