Amurka ba ta da kwarewa, inji Taliban

Hibatullah Akhundzada shi ne sabon shugaban Taliban a Afghanistan

Image caption

Hibatullah Akhundzada, tsohon shugaban kotunan Taliban, shi ne sabon shugaban kungiyar a Afghanistan,

Kungiyar Taliban ta mayar da martani kan matakin Shugaba Trump na yin watsi da yarjejeniyar zaman lafiya a Afghanistan, tare da fasa ganawar sirri da ya shirya yi da shugabannin kungiyar a Amurka.

Shugaban ya dauki matakin ne bayan wani wawan hari da kungiyar ta kai ranar Alhamis wanda ya hallaka mutane 12 ciki har da sojan Amurka daya.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Taliban ta kai hare-hare da dama a Afghanistan ciki har da na majalisar dokokin kasar a watan Yuni na 2015

A martanin kungiyar ta ce matakin shugaban ya nuna rashin kwarewa da kuma aniyar Amurka kan rikicin na Afghanistan;

A martanin nata kungiyar Taliban ta ce komai na tafiya lami lafiya kafin Shugaba Trump ya soke ganawarsu.

A sanarwar da kungyar ta fitar ta ce, an gayyaci shugabanninta zuwa Amurka a karshen watan Agusta, amma suka jinkirta har sai an kammala sanya hannu a yarjejeniyar da ake yi. Haka su ma kasashen yankin sun mara baya ga hakan.

Kungiyar ta ce tun da yanzu shugaban Amurkar ya soke tattaunawar zaman lafiyar, Amurka ce za ta fi yin asara, za ta rasa kimarta, sannan a yanzu za a kara sanin matsayi da manufarta kan batun zaman lafiya, wato za a san cewa ba da gaske take ba.

Image caption

Akwai kungiyoyin mayaka daban-daban na Taliban

A sanarwar Taliban ta ce, a bangarensu, sun tabbatar cewa, yaki dai kai musu shi aka yi, kuma a duk lokacin da ake da niyyar tattaunawa, a shirye suke.

Ta ce ficewa daga tattaunawar zaman lafiya kafin sanya hannu a yarjejeniyar, saboda hari ko fashewa daya kawai, hakan ya nuna rashin hakuri ko kwarewar Amurka, musamman ma a lokacin da rayuka da dukiyar tarin ‘yan Afghanistan suka salwanta a sanadiyyar hare-haren Amurka da kawayenta a Afghanistan.

Taliban din ta ce, tana da kwakkwarar manufa da zaman lafiya, domin shekara ashirin baya ta ce ta nemi a zauna a tattauna, kuma har a yau din nan a shirye take da hakan.

A karshe sun ce sun yi amanna, nan ba da jimawa ba Amurkawan ma za su cimma wannan matsaya.

Matakin na Shugaba Trump ya kasance tamkar wata babbar mahangurba ga shirin wanzar da zaman lafiyar a Afghanistan, matakin da harin da ‘yan Taliban suka kai wanda ya harzuka shugaban kasancewar akwai sojan Amurka daya tilo daga cikin mutum 12 da harin na Kabul ya hallaka a ranar Alhamis.

Tattaunawar yarjejeniyar dai na wakana lafiya kalau, da har da dama daga jama’ar Afghanistan na murna da ganin ana dab da kawo karshen rikicin da kusan a kullum ke musu taannati na rayuka da dukiya da zaman lafiya shekara da shekaru.

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...