Ambaliya ta yi ɓarna a Gombe

Akalla gidaje 100 ne suka lalace sannan mutane 500 sun rasa matsuguni bayan ruwan sama na ranar Juma’a a jihar Gombe.

Lamarin wanda ya faru a unguwar Dogon Ruwa da ke karamar hukumar Kaltungo, ya kuma tafi da awaki 15.

Shugaban gargajiyar yankin, Aliyu Isah, ya bayyana cewa daga cikin dabbobin guda 15 akwai tumaki da awaki, inda ya kara da cewa ambaliyar ta yi mummunar barna ga mutanen.

Isah, wanda shi ne Sa’in Dogon Ruwa, ya shaida wa ƴan jarida cewa, mahukuntan karamar hukumar sun sani kuma har yanzu ba su dauki mataki ba.

Ya yi kira ga gwamnatin jihar Gombe da ta taimaka musu.

More from this stream

Recomended