
Rundunar ’yan sandan jihar Neja ta kama wata mata mai suna Mariya Abdullahi bisa zargin sanya wa ’ya’yan kishiyarta guda 2 guba a garin Takuti da ke ƙaramar hukumar Lapai, lamarin da ya yi sanadin mutuwar ɗaya daga cikin yaran.
Rahotanni sun nuna cewa yaran, masu shekaru 4 da 9, sun sha wani ruwa da ake zargin guba ne daga cikin ƙoƙon da Mariya ta ba su.
Ɗaya daga cikin yaran ta rasu jim kaɗan bayan shan ruwan, yayin da aka garzaya da ɗayar zuwa babban asibiti, inda take karɓar magani a lokacin da aka haɗa rahoton.
An ce lamarin ya faru ne ranar Juma’a, 6 ga Nuwamba, 2026, bayan da ake zargin Mariya ta ba yaran ruwan bisa shawarar wata ƙawarta.
A yayin tambayoyi da ’yan sanda suka yi mata a ofishin Lapai, matar ta bayyana cewa ta aikata hakan ne saboda ba ta haifa wa mijinta ɗa ba, kuma ƙawarta ce ta rinjaye ta.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin ranar Asabar, inda ya ce an kama matar kuma tana fuskantar tambayoyi.
A cewarsa, jami’an ’yan sanda sun isa wurin bayan samun rahoton, inda suka tarar da yaran 2 a sume sakamakon shan abin da ake zargin guba ne. An garzaya da su wani asibiti na kusa, amma ɗaya ta mutu kafin ta samu kulawar likitoci.
Abiodun ya ƙara da cewa za a tura wadda ake zargin zuwa sashen binciken manyan laifuffuka na jihar (SCID) da ke Minna domin zurfafa bincike da kuma gurfanar da ita a gaban kotu.