’Yan Bindiga Sun Sace Ɗaliban Makarantar Islamiyya 14 a Jihar Neja



Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun yi awon gaba da ɗaliban makarantar Islamiyya guda 14 a yankin Pandogari, ƙaramar hukumar Rafi ta Jihar Neja.

Rahotanni sun bayyana cewa an sace ɗaliban ne ranar Asabar a lokacin da suke taimaka wa malaminsu wajen girbin masara a gonarsa da ke ƙauyen Tungan-Bako.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin, inda ya fayyace cewa adadin ɗaliban da aka sace 14 ne, ba 50 ba kamar yadda wasu rahotanni suka bayyana.

Ya ce jami’an tsaro na haɗin gwiwa sun fara ƙoƙarin ceto ɗaliban domin tabbatar da an kuɓutar da su daga hannun waɗanda suka sace su.

A cikin sanarwar da ya fitar, Abiodun ya ce rahoton farko da suka samu ya nuna cewa ɗaliban makarantar Islamiyya ne da ke taimaka wa malaminsu wajen girbin masara a gonarsa kafin aukuwar lamarin.

Ya ƙara da cewa jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da aikin ceto, kuma za a sanar da jama’a duk wani sabon ci gaba da aka samu.

Loading

Signing-in 3 seconds...

Signing-up 3 seconds...