Ƴan Bindiga Sun Kashe Jami’in ’Yan Sanda da Fararen Hula 11 a Kebbi

Muhammadu SabiuHausa15 minutes ago



Wasu da ake zargin ’yan ta’addar Mamudawa/Lakurawa ne sun kashe wani sufeto na ’yan sanda da fararen hula 11 a hare-haren da suka kai ƙauyukan Waiwayi da Kystu da ke ƙaramar hukumar Koko-Besse a Jihar Kebbi.

Rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce jami’in ya rasa ransa ne yayin musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da maharan.

Mai magana da yawun rundunar, SP Bashir Usman, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa ta wayar tarho.

Usman ya ce har yanzu ba a bayyana sunan jami’in da aka kashe ba, saboda ana jiran kammala binciken da ake gudanarwa.

Ya ce: “Eh, an kai hari ƙauyukan Waiwayi da Kystu daga wasu da ake zargin Mamudawa ne, kuma abin takaici, an kashe wani sufeto na ’yan sanda yayin musayar wuta. Ba zan iya bayyana sunansa ba har sai mun kammala bincike.”

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun ƙona gidaje tare da kwashe kayan abinci daga wasu shaguna a yankunan da abin ya shafa.

Hare-haren sun kuma tilasta wa mazauna ƙauyukan barin gidajensu domin neman mafaka a wuraren da suke ganin sun fi aminci.

Kakakin ’yan sandan ya ce jami’an rundunar tare da sauran hukumomin tsaro sun kewaye yankunan da aka kai wa hari domin hana sake aukuwar irin wannan lamari.

Ya ƙara da cewa jami’an tsaro sun fara farautar waɗanda suka kai harin domin kamo su.

Wannan hari ya ƙara jefa damuwa kan matsalar tsaro a wasu yankunan karkara na Jihar Kebbi, inda hare-haren ’yan bindiga ke ci gaba da barazana ga rayuka, dukiyoyi da zaman lafiyar al’umma.

Loading

Signing-in 3 seconds...

Signing-up 3 seconds...