Tinubu zai tafi Saudiyya aikin Umrah a ranar Alhamis

Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja a ranar Alhamis zuwa Makkah kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Umrah.

Bayanin tafiyar shugaban ƙasar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da  Bayo Onanuga  ma bawa Shugaban ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabaru, ya fitar ranar Laraba.

Onanuga ya bayyana cewa wannan ziyara za ta bai wa Shugaba Tinubu damar yin nazari na ruhaniya, ibada, da kuma yi wa Najeriya addu’o’in zaman lafiya, haɗin kai, kwanciyar hankali, da ci gaba mai ɗorewa.

Sanarwar ta ƙara da cewa yayin da yake Makkah, Shugaba Tinubu zai gudanar da ibadun Umrah tare da rokon Allah ya ɗora Najeriya kan hanya madaidaiciya da yiwa ƙasar da mutanen ciki albarka.

“Kafin ya bar Abuja, Shugaba Tinubu zai ƙaddamar da wasu kayan aiki da Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta saya domin ayyukanta a ɓangaren shugaban ƙasa na Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe.”

Onanuga ya kuma ce ana sa ran Shugaba Tinubu zai dawo Najeriya a mako mai zuwa.

Loading

Signing-in 3 seconds...

Signing-up 3 seconds...