APC Ta Lashe Dukkan Zaɓukan Ƙananan Hukumomin Gombe

Jam’iyyar APC mai mulki a jihar Gombe ta lashe dukkan zaɓukan ƙananan hukumomi 11 da aka gudanar a ranar Asabar 27 ga watan Yuni.

Shugaban hukumar zaɓen jihar, Abdullahi Garba, ya bayyana cewa APC ta samu nasara a dukkan kujerun shugabannin ƙananan hukumomi da kuma kujerun kansiloli 240 na jihar.

Ya bayyana zaɓen a matsayin babban ci gaba, musamman bayan faɗaɗa ƙananan hukumomin jihar zuwa gundumomin mulki 24.

A Najeriya, galibi jam’iyyar da ke mulkin jiha ce ke samun rinjaye a zaɓukan ƙananan hukumomi.

More from this stream

Recomended

Kotun Tarayya Ta Tabbatar Da David Mark A Matsayin Shugaban ADC

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta tabbatar da shugabancin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark. Kotun ta yi watsi da ƙarar da ɗan majalisar wakilai, Leke Abejide, ya shigar kan shugabancin jam’iyyar, inda ta bayyana cewa lamarin ya shafi harkokin cikin gida na jam’iyyar siyasa. Mai […]