Ƙungiyar Tinubu Vanguard Ta Janye Goyon Baya Ga Shugaba Tinubu da APC

Wata ƙungiya mai goyon bayan Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, wacce aka sani da Tinubu Vanguard, ta sanar da dakatar da dukkan ayyukanta na siyasa tare da janye goyon bayanta ga Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC mai mulki.

Ƙungiyar, wadda ta ƙunshi mambobi daga jihohi 19 na Arewacin Najeriya da Babban Birnin Tarayya Abuja, ta bayyana wannan matsaya ne ta bakin Daraktan Janar ɗinta, Hon. Kamilu Abdullahi Abubakar Maiganji, yayin da yake jawabi ga mambobin ƙungiyar da ’yan jarida a wani taro na musamman.

A cewar Maiganji, matakin ya biyo bayan abin da ya kira sakaci da rashin kulawa daga gwamnati, tare da rashin karrama rawar da ƙungiyar ta taka a lokacin yaƙin neman zaɓe.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban ƙungiyar ya bayyana a ranar Litinin cewa duk da gudunmawar da Tinubu Vanguard ta bayar wajen nasarar zaɓe, mambobinta na ci gaba da fuskantar tsananin matsin rayuwa ba tare da samun wani tallafi ko kulawa daga gwamnati ba.

More from this stream

Recomended