Gwamnatin Rasha ta bayyana cewa ta bai wa Venezuela tabbacin samun cikakken goyon bayanta, a daidai lokacin da Amurka ke ci gaba da kai hare-hare da kuma ɗaukar matakai a yankin Caribbean.
Moscow ta ce ta nuna matuƙar damuwarta kan yadda Amurka ke ƙwace jiragen ruwa masu dakon man fetur daga Venezuela, a yayin wata tattaunawa ta waya da ministocin harkokin wajen ƙasashen biyu suka yi.
Rasha ta bayyana cewa irin waɗannan matakai na iya ƙara rura wutar rikici tare da kawo cikas ga zaman lafiya da kasuwanci a yankin.
Tun da farko, ƙasar China ta yi Alla-wadai da matakan da Amurka ke ɗauka na ƙwace jiragen ruwan Venezuela, inda ta ce hakan ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa.
Rasha Ta Bayyana Goyon Baya Ga Venezuela Kan Matakan Amurka

