
Gwamnatin tarayya ta ayyana ta ranakun Alhamis 25 ga watan Disamba da kuma Juma’a 26 ga watan Disambar 2025 a matsayin ranakun hutun bikin Kirsimeti.
Har ila yau gwamnatin ta kuma ayyana ranar Alhamis 01 ga watan Janairu na shekarar 2026 a matsayin ranar hutun shiga sabuwar shekara
An sanar da haka ne a cikin wata sanarwa da, Dr. Magdalene Ajani babbar sakatariyar dindin ta ma’aikatar cikin gida ta fitar ranar Litinin a madadin ministan ma’aikatar, Olabunmi Tunji-Ojo.
A cewar sanarwar ministan ma’aikatar ya yi kira ga yan Najeriya da suyi amfani da lokacin bikin shagulgulan wajen duba da koyi da dabi’un kauna, zaman lafiya, kaskan da kai da kuma sadaukarwa kamar yadda haihuwar Annabi Isa Alaihissalam ta koyar.
Tunji-Ojo ya kuma shawarci yan Najeriya daga kowane addini ko kabila da suyi addu’ar samun zaman lafiya, kyautatuwar sha’anin tsaro da kuma cigaban Æ™asa.
Ya kuma shawarci yan Najeriya da su kasance masu bin doka da oda da kuma zama a ankare saboda tsaro.

