Tinubu ya sanya wa jami’ar lafiya ta Azare sunan Sheikh Dahiru Bauchi


Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sauya sunan Jami’ar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Azare zuwa Jami’ar Sheikh Dahiru Usman Bauchi, domin karrama marigayi fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Bauchi.

Tinubu ya sanar da wannan matsaya ne a ranar Asabar yayin ziyarar ta’aziyya da ya kai wa gwamnatin jihar Bauchi da iyalan marigayi malamin. Ya bayyana Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin mutum mai son bil’adama, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyar da ilimi da bin tafarkin Allah.

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yabawa shugaban ƙasar bisa ziyarar ta’aziyyar, yana cewa hakan alama ce ta girmamawa ga marigayi malamin, iyalansa da al’ummar jihar. Haka kuma, iyalan Sheikh Dahiru Bauchi sun nuna godiya ga shugaban ƙasa bisa jajircewarsa da kuma tura manyan jami’ai wajen jana’izar marigayin.

Bayan kammala ziyarar, shugaban ƙasar ya tashi zuwa Lagos ta filin jirgin sama na Sir Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.

More from this stream

Recomended