Sojoji sun kama motoci biyu dake kaiwa mayakan ISWAP kayayyaki

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun kama wasu motocin akori kura biyu dake dauke da wasu kayayyakin da ake zargin za su kai wa mayakan kungiyar ISWAP ne.

A cewar Zagazola Makama dake wallafa bayanan tsaro akan yankin tafkin Chadi an kama kayan ne biyo bayan gamsassun bayanan sirri da aka samu daga wasu mutane kan yadda aka dauko kayan daga Dapchi ya zuwa yankin Magumeri a jihar Borno.

Makama ya ce sojojin shiya ta biyu dake aiki tare da Civilian JTF ne su ka tsayar da motocin tare da tsare direbobinsu domin kara yi musu tambayoyi.

Ya kara da cewa kayan da aka samu a motocin sun hada da safayar taya guda 31, kangarwa guda 21, keken hawa biyu, buhun fulawa biyu da kuma katifa É—aya.

Sauran kayan da aka samu a motocin sun hada da doya guda 34, barguna biyu,buhun gawayi guda biyar, ledoji biyu dake dauke da garin kwaki, kayan yara da na manya, wayoyi hannu guda 6, power bank da kuma har 92,000.

More from this stream

Recomended