
Aƙalla mutane 15 ne suka mutu wasu 10 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya faru a garin Chiromawa, dake kan titin Kano zuwa Zariya.
Hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 03:20 na rana Alhamis.
Rahotanni sun bayyana cewa hatsarin ya rutsa da wata farar mota ƙirar Toyota mai namba NSR 188 KP dake ɗauke da mutane 25 da kuma wata babbar mota ƙirar Daf mai namba KMC 158 XW da aka ajiye ta a gefen titi.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa direban motar wanda ba a bayyana sunansa ba ne yaci karo da babbar motar ta baya bayan da motar ta ƙwace masa.
Sakamakon haka ne dukkanin fasinjojin da suke ciki suka jikkata.
Jami’an bayar da agajin gaggawa sun garzaya da mutanen ya zuwa babban asibitin garin Kura inda aka tabbatar da mutuwar direban motar da wasu fasinjoji 14 yayin da sauran fasinjoji 10 suka cigaba da samun kulawar likitoci.