Ƴan sanda sun ceto ɗaliban jami’a biyu da aka yi garkuwa da su a jihar Nasarawa

Rundunar ƴan sanda a jihar Nasarawa ta ce jami’anta sun samu nasarar ceto ɗalibai biyu na Jami’ar Tarayya ta Lafia da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su.

A wata sanarwa da aka fitar ranar Talata, Rahman Nansel mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar ya ce an yi garkuwa da ɗaliban ne a ranar 30 ga watan Maris.

” A ranar 30 ga watan Maris mun samu kiran kai ɗaukin gaggawa kan hari da aka kai gidanen kwanan dalibai dake bayan Nasara Estate a Tudun Kauri dake Lafia,” a cewar sanarwar.

” A lokacin harin an yi awon gaba da ɗalibai biyu na Jami’ar Tarayya dake Lafiya Sadiq Adinoyi da Sakina Adinoyi,”

Nansel  ya ce biyo bayan bincike da kuma bin diddigi da ƴan sanda suka yi an gano cewa masu garkuwar suna tsare da daliban a wani daji  dake bayan rukunin gidaje na  500 Estate dake kan titin zuwa Doma.

Ya ƙara da masu garkuwar sun tsere sun bar ɗaliban bayan musayar wuta da jami’an tsaro amma an samu nasarar kama ɗaya daga ciki mai suna Ibrahim Musa da ya fito daga ƙauyen Abuni a ƙaramar hukumar Awe ta jihar.

More from this stream

Recomended