
Hukumar kula da kiyaye afkuwar hatsura ta ƙasa FRSC shiyar jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu a hatsarin motar da ya faru a jihar ya karu zuwa mutane 23.
A ranar Juma’a ne wata motar tirela dake ɗauke da dabbobi da mutane ta ƙwace ta faɗi a gadar sama ta Muhammadu Buhari dake kan titin Maiduguri a birnin.
A wata sanarwa ranar Juma’a, Abdullahi Labaran mai magana da yawun hukumar a jihar ya ce mutane 48 ne suka jikkata a hatsarin.
Labaran ya ce tukin ganganci da direban yake yi shi ne ya jawo motar ta ƙwace ta faɗi abin da ya haifar da asarar rayuka da dukiya.
Jumillar mutane 71 ne hatsarin ya rutsa da su a cewar sanarwar da hukumar ta fitar.