Jam’iyya mai mulki a Najeriya APC ta taya tsohon mataimakin Shugaban kasar Atiku Abubakar murna bisa tsayar da shi takarar shugabancin a karkashin jam’iyyar adawa ta PDP.
A wata sanarwa da jam’iyyar APC ta fitar ta yi zargin cewa “tsohon shugaban kasar ya yi amfani da kudi ne wajen sayen kuri’un mambobin jam’iyyar don su sayar da shi takara.
“Shugabancin Najeriya ba na sayarwa ba ne,” in ji APC.
Daga nan ne sai jam’iyyar APC ta ce: “Atiku wanda hamshakin attajiri ne, ya yi amfani da kudi wajen sayen kuri’u wajen wakilan jam’iyyar PDP lokacin zaben fidda gwani na dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar wanda aka yi ranar Lahadi.”
Sai dai a wata sanarwa da ita ma jam’iyyar PDP ta fitar ta musanta zargin hakan, inda jam’iyyar ta ce “zarge-zarge marasa tushe ba za su taimaki Shugaba Buhari ba.”
“Babu kamshin gaskiya zargin da jam’iyyar APC ta yi cewa wadansu masu neman takarar shugabancin kasar a karkashin jam’iyyar PDP sun yi amfani da kudi wajen sayen kuri’u lokacin zaben fidda gwani,” in ji sanarwar da ta fito daga PDP.
A ranar Lahadi ne jam’iyyar PDP ta tsayar da tshon mataimakin shugaban kasar bayan ya samu nasara ne da kuri’u 1532.
An dai gudanar da zaben ne a Fatakwal, babban birnin jihar Rivers inda wakilai sama da 3,200 daga jihohin Najeriya 36 suka hallara domin zabar dan takarar da zai yi gogayya da shugaba Muhammadu Buhari.
Sauran ‘yan takarar da suka nemi kejarar shugabancin Najeriyar a jam’iyyar PDP, sun hadar da:
- Jonah Jang da ya samu kuri’u 19
- Datti Baba ya samu kuri’u 5
- David Mark ya samu kuri’u 35
- Turaki Taminu ya samu kuri’u 65
- Sule Lamido ya samu kuri’u 96
- Bafarawa ya samu kuri’u 48
- Hassan Dankwabo ya samu kuri’u 111
- Ahmed Markafi ya samu kuri’u 74
- Rabi’u Kwankwaso ya samu kuri’u 158
- Olubukola Saraki ya samu kuri’u 317
- Aminu Tambuwal ya samu kuri’u 693