Tarin magoya baya da kuma abokanan siyasar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Kwankwaso ne suka halarci taron lakca da aka shirya domin bikin cikarsa shekaru 68 a duniya.
Abokanai da kuma makusantan Kwankwaso da kuma Gidauniyar Kwankwasiya su ne suka shirya taron.
Manyan baƙin da suka halarci sun haɗa da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdulsalam da Shehun Malami Mallam Ibrahim Khalil.
Abdulrashid Garba tsohon mataimakin shugaban jami’ar Bayero kuma shugaban jami’ar Khalifa Sheikh Isyaka Rabi’u da kuma Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa shugaban jami’ar, Yusuf Maitama Sule dake Kano duk sun halarci taron. Ga wasu daga cikin hotunan wurin taron.