Wani mummunan hatsarin mota da ya faru a Gusau babban birnin jihar ya jawo asarar rayukan mutane 6 ƴan gida ɗaya.
Mutanen na tafiya ne akan babur lokacin da wata babbar mota tayi awon gaba da su a kusa da Gusau Hotel.
Mutanen da suka sun haɗa da wani magidanci matarsa da kuma ƴaƴansu huɗu.
Hatsarin ya girgiza mutane da dama dake birnin.
Kawo yanzu rundunar ƴan sandan jihar ta Zamfara bata fitar da wata sanarwa ba kan faruwar lamarin.