Wani mummunan hatsarin mota da ya faru a Gusau babban birnin jihar ya jawo asarar rayukan mutane 6 Æ´an gida É—aya.
Mutanen na tafiya ne akan babur lokacin da wata babbar mota tayi awon gaba da su a kusa da Gusau Hotel.
Mutanen da suka sun haÉ—a da wani magidanci matarsa da kuma Æ´aÆ´ansu huÉ—u.
Hatsarin ya girgiza mutane da dama dake birnin.
Kawo yanzu rundunar Æ´an sandan jihar ta Zamfara bata fitar da wata sanarwa ba kan faruwar lamarin.