NDLEA ta kama wani mai safarar hodar ibilis a filin jirgin sama na Kano

Jami’an hukumar NDLEA dake yaƙi da hana sha da kuma fataucin miyagun kwayoyi sun kama wani mutum mai suna, Okafor  Ifeanyi Anthony mai shekaru 38 a filin jirgin saman Mallam Aminu dake  Kano ɗauke da hodar ibilis lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa ƙasar Iran.

Mai magana da yawun hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi shi ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi inda ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar 15 ga watan Satumba.

Ya ce an kama Okafor ne lokacin da yake ƙoƙarin hawa jirgin Qatar Airways zuwa Doha kafin ya wuce Iran.

Babafemi ya ƙara da cewa Okafor ya kasayar da ƙullin hodar ibilis guda 76 da ya haɗiye a cikinsa bayan da ya shafe kwanaki uku a tsare ana sanya masa idanu.

More from this stream

Recomended