Abdulsalami ya kai ziyarar ta’aziyar mahaifiyar Yar’adua

Tsohon shugaban ƙasa,Abdulsalami Abubakar ya kai ziyarar ta’aziya ga iyalan Yar’adua, gwamnatin Katsina dama al’ummar jihar bisa rasuwar, Hajiya Dada Musa Yar’adua mahaifiyar marigayi shugaban ƙasa, Umar Musa Yar’adua.

Gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Umar Radda shi ne ya tarbe shi a filin jirgin saman  Umaru Musa Yar’adua dake Katsina.

A gidan gaisuwar tsohon shugaban ƙasar tare da rakiyar gwamnan jihar ta Katsina sun samu tarba daga Sanata Abdulaziz Yar’adua da sauran iyalan gidan na Yar’adua.

Abdulsalami ya yi addu’ar neman gafara ga marigayiyar tare neman Allah ya bawa iyalan haƙurin jure rashin da suka yi.

A wata yar gajeriyar hira da manema labarai, Abdulsalami ya ya bawa gwamnan jihar kan yadda ya samar dashi da zaman lafiya da tsaro a jihar.

More from this stream

Recomended