Osimhen ya koma Galatasaray da wasa

Ɗan wasan gaba na Najeriya, Victor Osimhen ya isa ƙasar Turkiyya inda zai fara buga wasa a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Galatasaray dake  ƙasar.

Da yake magana da manema labarai jim kaɗan bayan saukarsa a filin jirgin sama na Istanbul ya nuna murnarsa matuƙa kan irin tarbar da ya samu.

Dubban magoya bayan ƙungiyar ɗauke da ganguna  ne suka tarbe shi.

Ɗan wasan mai shekaru 25 ya koma ƙungiyar ne a matsayin aro daga ƙungiyar Napoli da yake buga wasansa acan bayan da dangantaka tayi tsami a tsakaninsu.

Ƙungiyar ta ƙasar Turkiyya za ta dauki nauyin biyan albashin Osimhen a tsawon lokacin aron  amma kuma babu tilashin sai sun saye shi a ƙarshen kakar wasannni.

More from this stream

Recomended