HomeHausaGwamnatin Kano ta janye dokar ta kaita zirga-zirga

Gwamnatin Kano ta janye dokar ta kaita zirga-zirga

Published on

spot_img

Gwamnatin jihar Kano ta janye dokar taƙaita zirga-zirga da aka saka a jihar biyo bayan ɓarna da sace dukiyar gwamnati da ta jama’a da aka yi a  lokacin da aka gudanar zanga-zanga kan halin matsin rayuwa da al’umma suke ciki.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Baba Halilu Ɗantiye shi ne ya sanar da janye takaita zirga-zirgar a cikin wani jawabi da aka watsa a kafafen yaɗa labarai a ranar Litinin.

A ranar 1 ga watan Agusta ne gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya sanar da saka dokar hana fita ta tsawon awanni 24 biyo bayan ɓarnar da aka yi a lokacin zanga-zangar.

A ranar 2 ga watan Agusta gwamnan ya sassauta dokar da awanni biyar domin bawa mutane damar gudanar da sallar Juma’a.

Kwamishinan ya ce gwamnan ya janye dokar bayan da ya gamsu cewa sha’anin tsaro ya inganta a jihar.

Ya ƙara da cewa yanzu mutane za su iya cigaba da gudanar harkokinsu na yau da kullum a cikin doka da oda.

Latest articles

Ƴansandan Najeriya sun hallaka ƴan fashi a Abuja

Rundunar 'Yan sandan Birnin Tarayya ta kashe wasu ‘yan fashi guda biyu yayin musayar...

Babban lauya Femi Falana zai nemi a biya diya ga yaran da aka sako

Babban lauya maikare hakkin bil'adama, Femi Falana  ya ayyana aniyarsa ta gabatar da buƙatar...

Buhari ya kai ziyarar jajen ambaliyar ruwa jihar Borno 

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ya kai ziyarar jaje jihar Borno. Buhari ya kai ziyarar...

Shettima ya gana da yaran da  aka sako a fadar Aso Rock

Yaran da aka gurfanar a gaban kotun kan zanga-zangar Endbadgovernance sun gana da mataimakin...

More like this