HomeHausaGwamnatin Katsina ta sassauta lokacin dokar hana fita

Gwamnatin Katsina ta sassauta lokacin dokar hana fita

Published on

spot_img

Gwamnatin jihar Katsina ta sassauta dokar hana fita da aka saka a jihar.

Dokar hana fitar da ta taƙaita zirga-zirga daga ƙarfe 07:00 na dare ya zuwa 07:00 na safe a yanzu an sassauta ta ya zuwa 10:00 na dare zuwa 10:00 na safe a dukkanin faɗin jihar .

Sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Garba Faskari ya sanar cewa mataimakin gwamnan jihar kuma mai riƙon muƙamin gwamnan jihr Mallam Faruk Lawal Jobe ya gamsu da rahotanni da yake samu na ingantar yanayin tsaro a ko’ina cikin jihar saboda haka ya bayar da umarnin rage wa’adin dokar ba tare da ɓata lokaci ba.

Mai riƙon muƙamin gwamnan ya yabawa jami’an tsaro yadda suka gudanar da aikinsu da kuma al’ummar gari ta yadda suka bada haɗin kai har gwamnatin ta shawo kan lamarin.

Latest articles

Ƴansandan Najeriya sun hallaka ƴan fashi a Abuja

Rundunar 'Yan sandan Birnin Tarayya ta kashe wasu ‘yan fashi guda biyu yayin musayar...

Babban lauya Femi Falana zai nemi a biya diya ga yaran da aka sako

Babban lauya maikare hakkin bil'adama, Femi Falana  ya ayyana aniyarsa ta gabatar da buƙatar...

Buhari ya kai ziyarar jajen ambaliyar ruwa jihar Borno 

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ya kai ziyarar jaje jihar Borno. Buhari ya kai ziyarar...

Shettima ya gana da yaran da  aka sako a fadar Aso Rock

Yaran da aka gurfanar a gaban kotun kan zanga-zangar Endbadgovernance sun gana da mataimakin...

More like this