Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan Yuni mai zuwa.

Dangote ya bayyana haka ne a wurin taron shugabannin kamfanoni da ake gudanarwa duk shekara a Kigali babban birnin Ruwanda.

Ya ce Najeriya za ta kawo ƙarsehn shigar da mai ƙasar a cikin watan Yuni lokacin da matatar mai ta Dangote za ta fara samar da tataccen man fetur.

“A yanzu haka Najeriya bata da dalili kowane irin na shigo da  mai fa ce man fetur nan da wani lokaci cikin watan Yuni nan da wasu sati huɗu ko biyar Najeriya bai kamata ta shigo da man fetur ba koda lita ɗaya ce,” ya ce.

Dangote ya ce za a shawo kan ƙarancin da ake samu na man fetur bama a Najeriya ba har da yammacin Afirka baki ɗaya.

Ya ce kawo yanzu suna samar da wadataccen man Diesel da yake isar Najeriya.

More from this stream

Recomended