Shugaban Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, Muhuyi Rimingado, ya ce wani bincike da aka gudanar game da bidiyon dala ma Ganduje.
Ya tabbatar da cewa faifan bidiyon da aka dauka na tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, yana karbar makudan kudaden daloli a matsayin cin hanci daga wani mutumi ɗan kwangila yana cusa su a aljihunsa gaskiya ne.
Bidiyon, wanda ya jawo hankalin jama’a sosai a shekarar 2017, ya kasance abin dubawa sosai.
Shekaru shida da faruwar lamarin, Shugaban Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, Muhuyi Rimingado, ya tabbatar da cewa ba ƙirƙirar bidiyon aka yi ba.
“An tabbatar da sahihancin bidiyon,” in ji Rimingado a ranar Laraba yayin wani taron tattaunawa na kwana daya kan yaki da cin hanci da rashawa a Kano.
Ya kuma amince da matsananciyar matsin lamba da ya fuskanta na tabbatar da rashin laifi ko laifin Ganduje tun bayan fitar da bidiyon.
Rimingado ya ci gaba da bayyana cewa tun a shekarar 2018 hukumar ta fara binciken zargin da ake yi wa Ganduje.
Sai dai kuma saboda kariyar da tsohon gwamnan ke da shi, tabbatar da laifinsa ko kuma ba shi da laifi ya zama kalubalen da ba za a iya magancewa ba.