Abubakar Aliyu kuma iyalansa su biyu ne suka rasu sakamakon wannan hastari na jirgin ruwa, kuma ya kara da cewa yanzu haka suna cikin tashin hankali sosai saboda aukuwar lamarin.
Shugaban karamar hukumar Ibbin Hon. Dr. Bala S. Bako ya tabbatar da faruwar hatsarin jirgin ruwan, ya kuma yi kira ga gwamnatin Jihar da ta tarayyya Nigeria da su kawo musu agajin gaggawa domin rayuwarsu na cikin hadari a yankin.
Yayin da muke hada wannan rahoton mun nemi jin ta bakin rundunar ‘yan sandan Jihar Taraba amma haka ba ta cimma ruwa ba.


