Jirgin Max Air ya fara aikin kwaso yan Najeriya daga Ukraine

Biyo bayan ware zunzurutun kudi har dalar Amurika miliyan 8.5 da gwamnatin tarayya ta yi domin kwaso yan Najeriya da yakin kasar Ukraine ya shafa yanzu haka kamfanin jirgin Max Air ya fara aikin kwaso su.

Jami’in yada labarai na kamfanin MAX Air Ibrahim Dahiru ya ce jirgin da suka tura Romania domin kwaso mutanen na da girman da zai iya daukar fiye da fasinja 500.

Dahiru ya ce zuwa safiyar jumma’ar nan a ke sa ran dawowar jirgin don an kammala rajistar fasinjojin da zai dauko da hakan ya nuna ba a fargabar samun wani jinkiri.

Kazalika Dahiru ya ce iya aikin da a ka ba wa kamfanin na zuwa Romania ne.

Daliban da sauran ‘yan Najeriya na kasashe da ke makwabtaka da Ukraine da su ka hada da Poland, Romania, Slovakia, Hungary har ma da wasu da su ka makale a yankin da Rasha ke da shi.

More from this stream

Recomended