Jami’an gwamnati a jihar Colorado sun sanar da cewa wani mutum dauke da bindiga ya kashe mutum shida yayin wata liyafar zagayowar shekarar haihuwa da aka yi a karshen mako saboda ba a gayyace shi ba.
‘Yan sanda sun ce Teodoro Macias mai shekara 28 ya harbe budurwarsa Sandra Ibarra-Perez mai shekara 28 da ‘yan uwanta biyar kafin daga baya ya harbe kansa da kansa da bindigar da ya ke dauke da ita.
Wannan lamarin ya auku ne a wani gidan tafi da gidanka da ke Colorado Springs da sanyin safiyar Lahadi.
Bikin an shirya shi ne domin wasu ‘yan uwan budurwar su uku, amma uku cikinsu sun rasa rayukansu a harin.
Wannan harin ya auku ne kasa da wata biyu bayan wani harin irin wannan da aak yi a wani shago da ke birnin Boulder na jihar ta Colorado wanda ya yi sandiyyar mutuwar muum 11.
Yan sanda sun kuma ce ɗan bindigan na fama da matsalar “mallakar abin da yake ƙauna”, kuma an san shi da tsananin kishi.
Ranar Talata ƴan sanda sun bayyana sunayen sauran mutum biyar da su ka rasa rayukansu a harin, kowanne da shekarunsa na haihuwa:
- Melvin Perez, 30
- Joana Cruz, 53 (Melvin’s mother)
- Jose Gutierrez Cruz, 21 (Melvin’s brother)
- Mayra Perez, 32 (Melvin’s wife)
- Jose Ibarra (Mayra’s brother)
Yan sanda sun ce bai yi rajistar bindigar da ya aikata wannan aika-aikar ba.
(BBC Hausa)