Ƴansandan Najeriya sun gayyaci shugaban NLC Joe Ajaero zuwa ofishinsu a Abuja

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta gayyaci shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasar (NLC), Joe Ajaero zuwa ofishinta a Abuja.

Rundunar ta gayyace shi ne dai saboda amsa tambayoyi game da zargin ɗaukar nauyin ta’addanci da cin amanar ƙasa da laifukan intanet.

Rundunar ta bayyana haka ne a wata takarda da ta aike wa Mr Ajaero ranar Litinin kamar yadda ƙungiyar NLC ta bayyana a shafukanta na intanet.

‘Yan sandan sun umarci shugaban ƙungiyar ƙwadagon ya hallara a ofishinsu da ke bincike kan bayanan sirri ranar Talata a Abuja domin amsa tambayoyi, suna masu gargaɗin cewa za a bayar da sammacin kama shi idan ya ƙi bin umarninsu.

More from this stream

Recomended