
Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta ce wasu mutane uku aka kashe da ake zargin masu garkuwa da mutane ne lokacin da suke ƙoƙarin yin garkuwa da mutane akan hanyar Dustinma zuwa Ƙanƙara.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar na cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 4:30 na yamma.
Aliyu ya ce masu garkuwar da suka tsare hanyar na ɗauke da muggan makamai.
Ya ƙara da cewa jami’an ƴan sanda sun isa wurin akan lokaci inda suka shiga musayar wuta da ƴan bindigar kuma suka kashe ƴan uku nan take.
Masa’udu Saidu jami’i a kungiyar ƴan bijilante ya samu raunin harbin bindiga a hannu kuma yana samun kulawa a asibiti a cewar mai magana da yawun rundunar ƴan sandan.