Ƴan sanda sun kama wani mutum da buhun tabar wiwi 15

Rundunar ƴan sandan jihar Nasarawa ta ce ta kama wani mai safarar miyagun kwayoyi tare da motar da yake aiki da ita ɗauke da buhuna 15 da ake zargin na ganyen tabar wiwi ne.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Lahadi mai ɗauke da sahannun mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, DSP Rahman Nanse  wacce aka rabawa manema labarai a ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce rundunar ta kama mutumin mai suna Saturday Gabriel ɗan shekara 43 ranar 31 ga watan Satumba da misalin ƙarfe 01:00 na rana a yayin da ɗaya wanda suke tare da shi ya tsere.

Ya ƙara da cewa an riƙe motar ƙirar Toyota Camry mai  rijistar namba KSF 843 FN dake ɗauke da buhunan 15 na ganyen tabar wiwin a matsayin shedar da za a gabatar a gaban kotu.

More from this stream

Recomended