
Ƴan sanda a jihar Adamawa sun kama wani mutum, Aminu Abubakar ɗan shekara 56 da ya kashe matarsa.
Abubakar mazaunin unguwar Lelewaji a rukunin gidaje na Shagari Phase 2 dake Yola a karamar hukumar Yola South ana zargin sa da dukan matarsa har ta kai ga ta mutu bayan da ya samu labarin ta na shirin yin aure.
Ana zargin cewa Abubakar ya saki matar tasa saki biyu amma kuma ya bata wurin zama har sai ta kammala idda.
Amma kafin ta kammala sai ya samu labarin cewa ta na shirin auren wani mijin na daban abin da ya harzuƙa shi har ta kai ga dukan da ya yi ajalinta.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Adamawa ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar.