Ƙungiyoyin ƙwadago sun dakatar da yajin aikin na wani dan lokaci bayan Ribadu ya shiga tsakani

Kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC da TUC sun dakatar da yajin aikin da suke yi a fadin kasar na wani dan lokaci sakamakon shiga tsakani da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu ya yi.


Matakin da aka bayyana bayan taron na sa’o’i daya, ya nuna yadda kungiyoyin suka amince da kudurin Ribadu na magance matsalolinsu ba tare da nuna son kai a siyasance ba.

Mataimakin shugaban TUC na kasa, Tommy Etim, ya bayyana cewa dakatarwar na wucin gadi ne, har zuwa lokacin da gwamnati za ta amsa bukatunsu.

Yajin aikin dai ya samo asali ne sakamakon cin zarafi da aka yi wa shugaban kungiyar NLC, Joe Ajaero, a lokacin wata zanga-zanga a jihar Imo.

Al’ummar kasar na jiran karin bayani yayin da dakatarwar ta wucin gadi ta ta’allaka ne kan ayyukan gwamnati cikin wa’adin da aka kayyade.

More from this stream

Recomended