Zanga-zanga da yajin aikinmu sai sun game Nigeria – ‘Yan Kwadago

Nigerian labour protest

Ma’aikatan kwadagon sun ce bayan zanga-zangar wuni daya a biranen kasar, za kuma su shiga yajin aikin sai-baba-ta-gani

Hadaddiyar kungiyar kwadago a Najeriya, United Labour Congress Of Nigeria, ta ce ta daura damarar gudanar da wani yajin aiki na sai Baba-ta-gani, don matsa lamba ga gwamnatocin kasar su amince da karin albashi mafi karanci na naira dubu talatin.

kungiyar ta umarci ‘ya’yanta a duk fadin Nijeriya su tashi da haramar fara wannan yajin aiki tun a tsakar daren jiya, da kuma wata gagarumar zanga-zanga da za a yi a duk fadin kasar.

Al’amarin na zuwa ne da nufin nuna rashin gamsuwa da matakin gwamnatin kasar a kan mafi karancin albashi.

Sakataren tsare-tsare na hadaddiyar kungiyar kwadago ta ”ULCN”, Kwamadred Nasir Kabiru Ahmad kuma jagoran zanga-zangar ta ranar Talata, ya ce sun umarci duk ‘ya’yansu su zauna a gida, wadanda suka fito kuma za su “zunduma zanga-zanga a duk fadin kasar”.

Hakkin mallakar hoto
PresIDENCY

Image caption

Ma’aikatan kwadagon sun ce gwamnati na jan kafa ne da gangan har sai an shiga zabe a kasar

Ya ce kugiyoyin kwadagon kasar sun dauki wannan mataki ne saboda gazawar shugaban kasa na mika kudurin dokar biyan mafi karancin albashi ga zauren majalisun Najeriya.

A cewarsa bayan kwamitin bangare uku (Tripartite Committee) ya amince da albashin mafi karancin albashi na naira dubu talatin, sai ‘yan kwadagon suka ba wa shugaban kasa mako biyu don gabatar da kudurin gaban majalisa.

“Tun daga ranar da muka mika wa shugaban kasa wannan rahoto, bai kira mu ya nuna mana ci gaban da aka samu ba, bai kuma tura majalisar ba, in ji Kwamared Nasir.

Ya ce matakin ya kara jefa kananan ma’aikata da sauran ‘yan kwadago cikin kunci da matsin rayuwa.

“Mu abin da muka dauka (gwamnati) wani sabon salo ne na kawo jinkiri har majalisa ta shiga hutu, da ta shiga hutu, zabe ya zo, shi ke nan. Ka ga babu yadda za a saurari ma’aikata” in ji sakataren kwadagon.

Kwamared Nasir Ahmad ya ce tsawon shekara uku ke nan, ana maganar biyan mafi karancin albashin na naira dubu talatin. “Mene ne dubu talatin ga ma’aikacin Najeriya?”

“Mu, mun dauka wannan, rashin adalci ne kuma rashin tausayin ma’aikata ne a Najeriya,” a cewar jagoran kwadagon.

Ya kuma zargi gwamnonin Najeriya da zalunci don kuwa: “Mu, mun san suna da kudaden da suke karba wanda ba ma dubu talatin ba, in ma dubu hamsin ne, akwai kudin da za a iya biyan ma’aikata a jihohi.”

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miĆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaĆ™i da yiwa tattalin arzikin Ć™asa ne ya hana shi bayyana...