Zamantakewa: Matakan kyautata zaman aure don gujewa matsaloli

Bayanan bidiyo,
Bidiyon shirin Zamantakewa: Matakan gyara zaman aure

Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Zamantakewa wani sabon shiri ne na BBC Hausa da zai dinga lalubo mafita kan yanayzin zamantakewar mutane a bangarori daban-daban. Kuma a wannan kashi na farko, shirin ya fara ne da zamantakewar aure da yadda za a kyautata ta.

Kyakkyawar zamantakewa ita ce ginshikin dorewar zaman aure da samun kwanciyar hankali har ma ta kai ga samar da zuri’a mai tarbiyya.

Sai dai kash rashin kyawun zamantakewa a miliyoyin gidajen aure ta sa aurarraki sai mutuwa suke yi a kullum, al’umma kuma na lalacewa saboda gaza samar da iyali na gari.

A misali a jihar Kano, hukumar Hisbah ta ce aurarraki 631 ne suka mutu a shekarar 2020, yayin da wani bincike na Mujallar International Journal of Social Science and Humanity da aka yi a 2009 ya ce akwai sama da zawarawa miliyan daya da aurensu ya mutu a jihar.

Kazalika, Hajiya Sadiya Datti mai kula da shafin Pearls of the North a Facebook, ta shaida min cewa duk rana su kan sami ƙorafe-ƙorafen da ke da alaƙa da taɓarɓarewar zamantakewar aure a ƙalla 100 daga masu bin shafinsu.

A duk lokacin da aka ce an yi aure tsakanin mata da miji dole a dinga samun sabani, musamamn ganin cewa kowannensu ya fito daga gida daban-daban.

Al’adunsu da dabi’unsu dole su bambanta, amma kuma yana da matukar muhimmanci su san cewa hakuri da juna.

To amma me ya kamata a yi don samun kyakkyatwar zamantakewa?

Malamai da masana halayyar ɗan adam da ƙwarraru da dama sun fayyace tarin abubuwan da suka sa aurarraki ke mutuwa a arewacin Najeriya.

Daga cikin kuwa har da rashin sanin mene ne zaman auren kansa kafin a shige shi, wato rashin wayarwa da mutane kai kan yadda za su tunkari sabuwar rayuwar da ake fatan mutu ka raba.

A al’ummar Hausawa an fi mayar da hankali kan shirye-shiryen auren fiye da koya wa ma’auratan yadda za su zauna lafiya da juna.

A wannan zamanin ma ana ganin yadda kashe makuÉ—an kuÉ—aÉ—e ya zama abin gadara da lafahari a aure, kama dag akan shirya liyafa, da kayan lefe da kayan É—aki da kayan gara da dai sauransu.

Sai dai za a iya cewa babu laifi a baya-bayan nan ana samun ƙaruwar buɗe cibiyoyin gyara zamantakewar aure a sassan yankin daban-daban.

Tun kafin a daura a aure a tabbatar da cewa an gabatar da sabbin ma’auratan ga irin waÉ—annan cibiyoyi ko wasu mutanen da aka san suna da Ć™warewa a hikimar zaman aure, don su É—ora su a layi na irin abubuwan da ya kamata su dinga yi.

Wasu labarai masu alaƙa

Abubuwa biyar masu muhimanci a zamantakewar aure

Duk halin da kuke ciki ku gaya wa juna, kar ka bari matarka ta ji wasu abubuwa da suka shafe ka a bakin wasu. Ko da aure za ka ƙara ya kamata ta fara ji daga bakinka ba a abakin wasu ba.

Ke ma duk abin da kike ciki ki tabbatar mijinki yana da masaniya, idan unguwa za ki je duk biye-biyen da za ki yi ki gaya masa kar ki bi bai sani ba a gano masa ke a kai labari.

Ku riƙe gaskiya da amanar junanku. Gaskiya ita ce wani sinadari da ake fara gina aure a kansa do samar da kyakkyawar zamantakewa.

Yarda da juna shi ne ginshiƙin ɗorewar zamanku tare, idan babu yarda to auren ko ya ɗore zai zama mai yawan raurawa.

Sannan riƙon amana jigo ne na kyautata zaman tarenku.

Girmama juna da mutuntawa

Ya zama wajibi ka girmama matarka da muradunta matuĆ™ar ba su kauce wa shari’a ba, sannan ita ma dole ta girmama ka da naka muradun.

Kar ku zama masu izgila wa juna da cin zarafi ko mutuncin juna da zagi da wulaƙanci. Wadannan halaye suna matuƙar ɓata zaman aure.

Ya kamata ma’aurata su san cewa kowane É—an adam na buĆ™atar girmamawa da mutuntawa.

Bayanan bidiyo,
Bidiyo: Cibiyoyin faÉ—akar da mutane kan zaman aure a Kano

Ya zama wajibi idan an aso zama ya yi dadi dukkan ma’aurata su sauke haƙƙoĆ™in junansu.

Namiji dole ne ya sauke aƙƙn da aka ɗora masa na ciyarwa da shayarwa da sutura da muhalli, kula da lafiyar iyali, ilimintarwa, sauke haƙƙin auratayya da kuma kyautatawa, kare mutuncinta.

Ke kuma mace dole ki sauke haƙƙoƙi kamar kula da dukiyar miji, kare jinsa da ganinsa daga abin da ba shi kenan ba, ta kiyaye martabarsa da mutuncinsa, ta kiyaye sirrinsa, ta kuma kyautata masa da sauran su.

Idan dai zaman aure ya haɗa ku to ku sani lallai kuna buƙatar nuna wa juna ƙauna da so. Su waɗnanan su ne turakun da za su ci gaba da zaunar da aurenku lafiya.

Kazalika duk ɗan adam na so idan ya yi abin kirki a yaba, musamman ma mata. Ku daure duk lokacin da abokan zamanku suka yi wata bajinta ko ta kwalliya ko girki ko ga su maza idan suka yi wata hoɓɓasa to a dinga yabon juna.

Sannan ku zama masu tausayawa juna a kowane irin yanayi, don tausayi na ƙara soyayya. Idan matarka na da ciki dinga nuna ka fi kowa tausaya mata, musamma ma a irin halin da suke shiga na laulayi.

Idan ta zo haihuwa ka kasance tare da ita. Haka ke ma ki zama mai yawan nuna tausayi ga mijinki musamman a lokutan da yake cikin wani yanayi na rashin daɗi ko kuma idan ya yi haƙilo ya kawo abubuwan buƙatar gida.

Za kuma ku so kallon

Sauran abubuwan da ya kamata ma’aurata su kiyaye kamar yadda Malama Halima Sani, wata mai sharhi kan zamantakewar aure a Kano ta faÉ—a, sun haÉ—a da:

  • Mutunta iyaye da dangin juna
  • Almubazzaranci da abubuwan da maigida ya saya don amfanin iyali da gida
  • A guji shashanci
  • A guji wulakanci
  • A guji raina juna
  • A guji saurin manta alkhairi
  • A guji tona asirin zaman aure
  • Ku guji rashin samar da manufa a rayuwar aure
  • Ku guji rashin tsari
  • Ku guji rashin iya Magana
  • Yawaita godiya
  • Hakuri da juna
  • Yi wa juna uzuri
  • Ba da damar tattaunawa.

[ad_2]

More News

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...

ĆŠan agajin Izala ya samu lambar yabo, kujerar hajji, kyautar mota bayan ya tsinci naira miliyan 100 ya mayar wa mai su

Salihu AbdulHadi Kankia, mamba ne na kungiyar agaji ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), ya samu yabo da tukuicin mayar da...

Musulmi a Zaria sun yi taron addu’o’i saboda mummunan halin matsi da Najeriya ke ciki

Musulmi a garin Zaria na jihar Kaduna, sun gudanar da addu'a ta musamman domin neman taimakon Allah kan halin da 'yan Najeriya ke ciki...