Zaben 2023: Ko Tafiyar Win-Win Za Ta Iya Cin Zaben Gwamna A Kano ?

Win-Win Kano Sabuwa tafiyar ta matasa ce” wadannan sune kalaman, Engr Muazu Magaji Dansarauniya jagoran tafiyar gidan  siyasar da ake wa lakabi da Win-Win Kano Sabuwa a duk lokacin da ya karbi wasu mutane da suka kawo masa ziyara.

Engr Muazu Magaji


Burin wannan tafiya ta su bai wuce zamanantar da jihar Kano ba ta yadda birnin zai yi gogayya da sauran birane a duniya.


Duk da cewa jagoran tafiyar ya nuna sha’warsa ta gadar kujerar gwamnan Kano daga gwamna mai ci Abdullahi Umar Ganduje wasu mutane da dama suna ganin hakansa ba zai cimma ruwa ba ganin yadda akwai manyan yan takarkaru dake gabansa a jam’iyarsa ta APC.

Tinubu ko Osinbajo ina al’ummar Kano za su karkata?.
Atiku ya hadu da wasu jiga-jigan jam’iyar APC.


Biyo bayan rikicin da ya barke a jam’iyar APC inda a yanzu ake da shugabanci  tsagi biyu; shugabancin Abdullahi Abbas da gwamnatin jihar ke marawa baya da kuma na su Ahmadu Haruna Zago da yake samun goyon bayan sanata Ibrahim Shekarau, danmajalisar tarayya, Shaaban Ibrahim Sharada da sauransu.


Magaji ya zabi yin biyayya ga bangaren, Ahmadu Haruna Zago sai dai wasu na ganin cewa rara-gefe kawai yake ba shi da wani tasiri a tafiyar ta su.


“Idan ka duba zaka ga siyasa ya ke ta soki burutsu, yau ya taba wannan gobe wancan ba tare da wata alkibla guda daya ba. Duk da cewa yafi sukar gwamnati hakan baya rasa nasaba da sauke shi daga mukamin kwamishina da kuma na shugaban kwamitin aikin shimfida bututun iskar gas, “a cewar wani mai sharhi kan al’amuran yau da kullum.


Shi ma wani mai bibiyare siyasar jihar Kano ya ce “Dansarauniya ka iya zama dan hakin da ka raina a kakar zaben 2023.”
Lokaci ne kadai zai bayyana irin tasirin da tafiyar siyasar Win-Win Kano Sabuwa za ta yi a siyasar jihar Kano.

Author: Sulaiman Sa’ad
Email: info@arewa.ng

More News

2023: 7 APC aspirants battling for Oyo central senatorial district ticket

No fewer than seven aspirants on the platform of the All Progressives Congress (APC), have indicated interest to represent Oyo Central senatorial district in...

Kwankwaso ya ziyarci Obasanjo

Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo. Ziyarar ta Kwankwaso wani bangare ne na cigaba da tattaunawar...

Kwankwaso ya ziyarci Obasanjo

Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo. Ziyarar ta Kwankwaso wani bangare ne na cigaba da tattaunawar...

Sojojin sun kama tarin makamai a a hannun mayakan IPOB

Rundunar sojan Najeriya ta samu nasarar kama makamai da suka hada bindigogi hodar hada bam a jihar. Rundunar ta samu gagarumin wannan nasara ne biyo...