Tinubu ko Osinbajo ina al’ummar Kano za su karkata? – Sulaiman Sa’ad

Tun bayan da aka shiga sabuwar shekarar 2022 wacce daga ita sai kakar babban zaben shekarar 2023 al’amura suka fara kankama kan shirye-shiryen zaben.


Lamarin dai yafi kamari a jam’iyar APC mai mulki inda yan takarkaru da dama suke ta jirwaye mai kamar wanka game da yiyuwa ko kuma akasin tsayawar su takara.

Tinubu ko Osinbajo


Kawo yanzu dai mutane biyu su aka fi an bato kan batun tsayawa takarar shugaban kasa a jamiyar APC wato tsohon gwamnan Lagos Bola Tinubu da kuma mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.
Da alama dai guguwar zaben na shekarar 2023 ta fara tasowa daga Kano ganin yadda wasu jiga-jigan yan siyasa daga jihar suka fara bayyana goyon bayansu ga Tinubu da kuma Osinbajo.


Tsohon danmajalisar tarayya, Abdulmumin Jibrin Kofa shi ne ya fara bayyana goyon bayansa ga Tinubu a yayin wani taron gangamin addua’a da ya shirya domin samun nasarar Tinubu a zaben na 2023.
Shima danmajalisar tarayya dake wakiltar mazabar Tarauni, Hafiz Kawu ya bayyana cewa Osinbajo ne mutumin da ya fi dacewa ya gaji shugaban kasa,Buhari.


A baya dai jama’ar Kano sun koka kan yadda ake watsi da su da zarar an samu nasarar zabe duk da irin yawan kuri’ar da suka bawa shugaban kasa, Buhari da kuma jam’iyarsa ta APC.
Abin jira a gani ko a bana za ta sauya zani. – Sulaiman Saad

More News

Yan bindiga sun kai hari kan ofishin yan sanda a Kogi

Da tsakar daren ranar Juma'a ƴan bindiga suka kai hari kan ofishin shiya na yan sanda dake Eika Ohizenyi a karamar hukumar Okehi...

Yan bindiga sun kai hari kan ofishin yan sanda a Kogi

Da tsakar daren ranar Juma'a ƴan bindiga suka kai hari kan ofishin shiya na yan sanda dake Eika Ohizenyi a karamar hukumar Okehi...

2023: Why I didn’t reject Atiku’s request to be his running mate – Gov Okowa opens up

The Governor of Delta State, Ifeanyi Okowa, has given reasons he accepted to be running mate to the presidential candidate of the Peoples Democratic...

Yan bindiga sun yi garkuwa da DPO a Nasarawa

CSP Haruna Abdulmalik DPO na yan sanda dake karamar hukumar Nasarawa Eggon a jihar Nasarawa ya fada hannun masu garkuwa da mutane. Babban jami'in ɗan...