Za mu sake bitar mafi karancin albashi a Najeriya—Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya yi alkawarin sake nazarin mafi karancin albashin ma’aikata domin dacewa da yanayin tattalin arzikin kasar nan.

A cewarsa, akwai bukatar gwamnatin tarayya da na jihohi su duba mafi karancin albashi tare da kuma karfafa tushe da aiwatar da kudaden shigar kasar.

Ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a lokacin da yake ganawa da ‘ya’yan kungiyar gwamnonin Progressive Governors’ Forum, wadanda suka bayyana goyon bayansu ga shugaban kasar kan cire tallafin.

Da yake magana a lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kungiyar, Tinubu ya ce, “Muna bukatar yin wasu kididdiga da bincike kan mafi karancin albashi,” ya kara da cewa, “Dole ne mu duba hakan tare da kuma kudaden shiga. Dole ne mu karfafa tushe da kuma amfani da kudaden shigar mu.”

More News

An samu ambaliyar ruwa a Adamawa

Anguwan Tana, al’ummar karamar hukumar Yola ta Arewa, sun shiga tasgaro a ranar Alhamis sakamakon ambaliya daga kogin Kilange da kogin Faro. Mazaunan garin...

Sojoji sun ceto mutane 6 daga cikin ɗaliban jami’ar Gusau da aka sace

Sojoji sun ceto dalibai mata shida daga cikin daliban Jami'ar Gwamnatin Tarayya dake Gusau da aka bada rahoton yan bindiga sun yi garkuwa da...

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da ɗaliban Jami’ar Tarayya da ke Gusau

An sace wasu daliban jami’ar tarayya ta Gusau da ba a tantance adadinsu ba da sanyin safiyar Juma’a. ‘Yan ta’addan masu yawan gaske sun...

Ƴan sanda sun kama masu safarar makamai wa ƴan bindiga

Jami’an hukumar ‘yan sanda reshen Karasuwa a jihar Yobe sun cafke wasu mutane biyu da ake zargi da kai wa ‘yan bindiga makamai da...