Za a rufe Gasar Hikayata ta 2019 | BBC Hausa

Hikayata

Da karfe goma sha biyu na daren Juma’ar nan ne ake sa ran rufe Gasar Kagaggun Labarai ta BBC Mata ta BBC Hausa, wato Hikayata, ta bana.

Hakan dai na nufin daga wannan lokacin, duk labarin da aka aiko ba zai samu shiga gasar ba.

“Za mu sa rariya mu fara tace wadannan labarai da muka samu”, inji Shugaban Sashen Hausa na BBC, Jimeh Saleh, wanda ya kara da cewa, “idan muka tace wadannan labarai muka ga wadanda suka cancanta a tura wa alkalan…sai mu tura musu”.

Daga ranar Litinin 2 ga watan Satumba ne dai ake sa ran fara tantance labaran da nufin fitar da guda 25 wadanda za a tura wa alkalan gasar, su kuma su zabi ukun da suka fi fice da wadansu 12 da suka cancanci yabo.

Wannan ne dai karo na hudu da ake shirya wannan gasa, kuma a cewar Jimeh Saleh, kwalliya ta biya kudin sabulu.

“A kwanakin baya mun yi waiwaye adon tafiya, mun samu wadanda suka yi nasara bara, da bariya, da ma shekarar da muka fara, sun yi mana bayanin amfanin da suka samu da ma yadda gasar ta sauya rayuwarsu”.

Sai dai kuma, a cewar Jimeh, ba wannan ne ma’aunin nasarar gasar ba a wajen Sashen Hausa na BBC.

“Tun farko, bayanin da muka yi wa jama’a shi ne mun kirkiro da wannan gasar ne saboda mu bai wa iyayenmu mata damar fadin albarkacin bakinsu….

“Duk wadda ta turo da rubutunta, a wajenmu, gwarzuwar Hikayata ce, kuma marubuciya ce, kuma ta yi nasara…. Musamman idan ‘ya mace a kasar Hausa ta dauki alkalami ta fara rubutu, mu a wajenmu ta yi nasara”.

Daruruwan mata ne dai daga sassa daban-daban na duniya suka aiko da labaransu domin shiga gasar.

A karshen watan Oktoba ake sa ran bayyana gwarzuwar gasar ta bana, a kuma danka mata kyautar kudi da lambar yabo yayin wani biki a Abuja, babban birnin Najeriya.

Safiyya Jibril Abubakar ce ta lashe gasar a bara da labarinta mai suna ‘Ya Mace wanda labari ne na irin gwagwarmayar da ‘ya’ya mata ke sha a kasar Hausa sakamakon takure irin rawar da suke iya takawa a tsakanin al’umma.

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miĆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaĆ™i da yiwa tattalin arzikin Ć™asa ne ya hana shi bayyana...