Za a mayar da ƴan Najeriyar da suka maƙale a Saudiyya gida

'Yan ci rani a Saudiyya

Wani bidiyo da ake ta yaɗawa a shafukan sada zumunta ya nuna wasu da ake tunanin ƴan Najeriya ne da suka maƙale a Saudiyya.

Babu tabbas kan wanda ya naɗi bidiyon saboda bai nuna fuskarsa ba amma an jiyo muryarsa yana kira ga gwamnatin Najeriya ta kawo masu ɗauki.

“Ina miƙa gaisuwata da godiyata a gareku yan siyasar ƙasata da aka zaɓa. Burin wannan bidiyon shi ne don in nuna maku halin da mu ƴan Najeriya muke ciki a nan Saudiyya tsawon wata shidda,” a cewar mutumin wanda ya yi magana da harshen turanci.

Ya ci gaba da bayyana halin da suke ciki ba tare da ya nuna fuskarsa ba.

Sai sauran mutane da ke kwance a wani ɗaki mai faɗi inda mafi yawansu suka rufe jikinsu da wani abu mai kama da baƙar leda.

Mutanen na da yawa kuma duk da girman ɗakin akwai alamar a matse suke.

Mutumin ya bayyana cewa babu wanda ya yi masu bayanin lokacin da za a mayar da su ƙasarsu kamar yadda wasu ƙasashe suka ɗauke ƴan ƙasarsu daga Saudiyya.

“A ƙa’ida mako biyu ne ake ajiye mutane a nan sai a maida su gida amma sai gashi wasu daga cikinmu sun yi wata biyar, wasu shida wasu ma wata bakwai suka kwashe a wurin nan,” in ji mutumin.

Ya rufe bidiyon da waɗannan kalaman: “A madadin dukanmu da ke wurin nan don Allah a taimake mu, muna so a taimake mu, mu koma ƙasarmu.”

BBC ta samu tattaunawa da wanda ya ce shi ne ya fara fitar da bidiyon amma ya ce ba shi ne ya naɗa ba.

Ya ce ɗan uwansa mai shekara 28 na cikin ƴan Najeriya da aka ɗakko hotonsu a wannan ɗakin da ya ke zargin cewa ‘gidan yari’ ne.

Ya bayyana cewa wani kamfanin Najeriya ne mallakin ƴan Saudiyya ya nemi masu buƙatar yin aiki a Saudiyya don sama masu biza.

A dalilin haka ne ƙanin nasa ya biya kuɗi aka yi masa biza kuma ya tafi birnin Riyadh na Saudiyya inda ya samu aiki a wani wurin wanke motoci shekaru kimanin huɗu da suka wuce.

Sai dai ya ce ƙanin nasa ya samu matsala da uban gidansa inda daga nan ne ya sa hannu a takardarsa ta izinin zama a ƙasar wanda ke nuna cewa ya janye daga zama waliyyinsa a ƙasar.

Yin haka ke da wuya sai ƴan sanda suka kama shi tare da wasu abokanan aikinsa ƴan Najeriya da ƴan wasu ƙasashen wanda tuni ƙasashensu suka mayar da su gida.

Mutumin ya shaida wa BBC cewa shi ne ya sa aka naɗi bidiyon kuma ya yaɗa a shafukan sada zumunta don jawo hankalin hukumomin Najeriya.

Bayyanar bidiyon ke da wuya sai shugabar Hukumar da ke kula da harkokin ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje NIDCOM, Abike Dabiri-Erewa ta wallafa wani saƙo a shafinta na Twitter inda ta ce mutanen da ke cikin bidiyon ƴan Najeriya ne da suka shiga Saudiyya ba a bisa ƙa’ida ba.

Haka kuma, a saƙon Misis Dabiri ta yi wa ƴan ƙasar gargaɗin shiga wasu ƙasashe ba tare da bin ƙa’idojin da suka dace ba.

“Za a dawo da ƴan Najeriya da suka shiga Saudiyya ba a bisa ƙa’ida ba ranar 28 da 29 na wannan watan na Janairu idan shirin da muke yi ya tafi yadda muke so. Dama an samu tsaiko ne wajen ɗebo su saboda annobar korona,” kamar yadda ta wallafa.

Misis Dabiri-Erewa ta wallafa wannan bayanin ne bayan da hoton bidiyon ya riƙa yawo a shafukan sada zumunta kuma mutane su ka yi ta tambayarta idan tana da masaniyar halin da mutanen ke ciki.

A baya dai Hukumar NIDCOM ta sha ɗebo ƴan Najeriya da suka maƙale a wasu ƙasashe.

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...