Za A Kammala Kwashe Alhazan Najeriya Ranar Asabar

Hukumar Aikin Hajji Ta Kasa NAHCON ta ce za a kammala kwashe alhazan Najeriya zuwa kasar Saudiyya a ranar Asabar 24 ga watan Yuni.

A wata sanarwa da aka fitar ranar Alhamis, mataimakiyar daraktan yaɗa labarai a hukumar ta NAHCON, Fatima Usara ta ce dukkanin kamfanonin da suke aikin dakon ɗaukan alhazan za su kammala kafin ko kuma ranar Asabar.

Usara ta ce alhazan Najeriya sama da 71000 ne aka dauke su ya zuwa Madina da kuma Jeedah a kasar Saudiyya.

Ta shawarci maniyyata da har yanzu ba a tuntube su ba da su ziyarci ofisoshinmu hukumomin alhazai dake kusa da su domin gabatar da bayanan su da kuma tabbatar da lokacin tafiyarsu.

More from this stream

Recomended