Yan sanda sun kashe mayakan IPOB biyu a Anambra

Rundunar ƴansandan jihar Anambra,ta ce jami’anta sun kashe wasu yan bindiga biyu a da zake zargin ya’yan IPOB ne a kauyen Nkpor dake karamar hukumar Idemili ta jihar.

Yan bindigar ne cikin motoci biyu da kuma kan babur daya suka kai wa jami’an tsaron hari lokacin da suke gudanar da aikin sintiri akan titin Nkpor.

Mai magana da yawun, rundunar yan sandan jihar, DSP Ikenga Tochukwu a wata sanarwa ya bayyana cewa martanin da jami’an tsaro suka mayar shi ya halaka yan bindigar a musayar wuta.

Ikenga ya kara da cewa jami’an yan sanda sun samu nasarar kwato bindiga daya da kuma mota ɗaya a yayin da sauran batagarin suka samu nasarar tserewa.

More from this stream

Recomended