
Rundunar yan sandan jihar Anambra da haɗin gwiwar yan bijilante na jihar sanar da sun kashe masu garkuwa da mutane su biyu a wani farmaki da suka kai kauyen Ichida dake karamar hukumar Anaocha ta jihar.
Sabon kwamishinan yan sandan jihar, Mista Adeyemi Adeoye shi ne ya bayyana haka a wurin wani taron manema labarai a Awka babbar birnin jihar.
Ya ce jami’an tsaron sun samu nasarar ceto wata mace ba tare ta ji rauni ba farmakin da suka kai da misalin karfe 08:13 na daren ranar Talata.
Jihar Anambra na daga cikin jihohi yankin kudu maso gabas dake fama da matsalar tsaro sakamakon ayyukan