Yan sanda sun harbe yan fashi biyu a Akwa Ibom – AREWA News

Rundunar yan sandan jihar Akwa Ibom ta ce ta kashe wasu yan fashi biyu a wata musayar wuta da suka yi a kauyen Ifuhe dake karamar hukumar Ikot Ekpene ta jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sahannun jami’in hulda da jama’a na rundunar,SP Odiko Makdon da aka rabawa manema labarai ranar Juma’a a Uyo babban birnin jihar.

A cewar mai magana da yawun rundunar, yan fashin sun hangi motar jami’an tsaro lokacin da suke tsaka da aikata ta’asa a yankin inda suka budewa motar wuta abin ya jawo aka yi musayar wuta.

Ya kara da cewa akwai yiyuwar wasu daga cikin yan fashin sun tsere cikin dajin da raunin harbin bindiga a yayin da aka tabbatar da harbe mutane biyu kuma aka tabbatar sun mutu a asibitin yan sanda dake Ikot Ekpene.

More from this stream

Recomended