Yan sanda na cigaba da kokarin ceto daliban Islamiyyar Salihu Tanko

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce nan ba da jimawaba za ta samu nasarar kubutar da daliban Islamiyyar Salihu Tanko da aka sace a jihar Neja da ke hannunun ‘yan bindiga.

Kawo yanzu dai wadannan yara da yawansu ya haura sun shade makonni 11 a hannun wadannan ‘yan fashin daji ba tare da samun nasarar kubutar da su ba.

A wani taron masu ruwa da tsaki akan sha’anin tsaron a masarautar Kontagora sabon kwamishinan ‘yan sandan jihar Nejan Monday Bala Kuryas ya ce sun kara shirya jami’an tsaronsu, kuma nan ba da jimawa ba za su kwato yaran.

Gwamnatin jihar Nejan dai ta ce tana neman hadin kan jama’a musamman kabilar Fulani wajen yaki da bata garin dake cikinsu in ji kwamishinan kananan hukumomi da masarauta na jihar Barista Abdulmalik Sarkin Daji da ya wakilci gwamnatin jihar Neja a wajen taron.

Wakilin kabilar Fulani a taron sarkin Fulanin masarautar Kontagora Hardo Abubakar Badare yace sun shirya bada rayuwarsu domin samar da zaman Lafiya a yankin.

Masarautar Kontagora na daya daga cikin yankunan dake fama da matsalar ‘yan fashin daji masu satar shanu da yin garkuwa da jama’a domin neman kudin fansa dama, kisan jama’a babu gaira babu dalili.

More News

Yan bindiga sun sace shugaban karamar hukuma a jihar Nasarawa

Wasu yanbindiga sun yi awon gaba da shugaban karamar hukumar Keffi ta jihar Nasarawa, Muhammad Baba Shehu da direban sa. Yan bindigar sun samu nasarar...

‘Yarjejeniya da barayin daji ta zamar mana dole’

Ga alama al'ummomin wasu garuruwa a karamar hukumar Shiroro ta jihar Naija a Najeriya za su ci gaba da yarjejeniyar biyan 'yan bindiga domin...

Abuja-Kaduna train: We’re Still negotiating with bandits – FG

The Federal Government has assured Nigerians, especially relatives of kidnapped Abuja-Kaduna train attack victims, that negotiation with bandits is ongoing to ensure their safe...

Kwankwaso ya ziyarci Obasanjo

Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo. Ziyarar ta Kwankwaso wani bangare ne na cigaba da tattaunawar...