‘Yan Nijar ba sa maraba da ziyarar shugaban Faransa

Macron

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Wasu ‘yan kasar Nijar ba sa maraba da ziyarar shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, wadda ya shirya kai wa kaburburan sojojin Nijar 71 da suka mutu a farkon makon jiya.

Shugaban na Faransa yana kan hanyarsa ne ta zuwa birnin Abidjan na kasar Ivory Coast, inda zai yi bikin Kirsimati tare da dakarun kasarsa da ke cen.

Macron ya zabi ya yada zango a Nijar ranar Litinin, sai dai wasu ‘yan kasar da dama na kiraye-kirayen cewa Faransa ta tattara komatsanta ta bar kasar ta Nijar.

Faransa, wadda ita ce ta yi wa Nijar mulkin mallaka, har yanzu ta zaman uwar gijiyar Nijar kuma har yanzu tana koyi da salon mulkinta har ma da wasu dabi’u.

‘Yan Nijar din suna zargin uwar gijiyar tasu da raka barawo da kuma raka mabi-sawu a yakin da yankin Sahel ke yi da ‘yan bindiga.

“Ai tun 13 ga wannan wata ya kamata ya zo tun da ranar aka yi jana’izar sojojin amma bai zo ba,” in ji Alhaji Idi Amadou.

Ya kara da cewa: “15 ga watan nan shugabannin Sahel suka zo ta’aziyya, nan ma bai zo ba. Kwatsam sai muka ji zai je Cote d’Ivoire sannan ya ce zai zo nan.

“Ina ganin zuwansa yana da alaka da koke-koken ‘yan kasashen Sahel a kan Faransa.”

Ku latsa alamar lasifikar da ke kasa don sauraron rahoton Tchima Ila Isoufou daga Nijar kan batun:

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Rahoton Tchima Ila kan ziyarar da Macron zai kai Nijar

Sai dai Madam Aishatu Ummani tana da akasin wannan ra’ayi, inda ta ce “babu yadda wata kasa ta yanke hulda da sauran kasashen duniya”.

Aishatu Ummani ta ci gaba da cewa: “A yanzu idan aka hana ka bizar Faransa kuka za ka yi sannan kuma ‘ya’yanmu suna karatu a can.

“Tun kafin ‘yancin kai muke da kyakkyawar alaka da su. Kamar yadda mu ma idan wani abu ya faru muke kai ta’aziyya Faransa shi ma haka muke fatan ya zo lafiya ya koma lafiya,” in ji ta.

Zuwa yanzu gwamnatin Jamhuriyyar Nijar ba ta fito fili ta bayyana batun ziyarar ba.

Sai dai majiyoyin da ke kusa da gwamnatin na cewa Shugaba Macron ba zai dauki dogon lokaci ba a Yamai, zai yi ta’aziyya ne ya ziyarci kaburburan sojojin sai ya koma.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Yadda aka yi jana’izar sojojin Nijar 71

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...